in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An yi bikin wasanni a tsakanin matasan kasa da kasa karo na biyu a Guangdong dake kasar Sin
2017-04-27 10:47:35 cri

A kwanakin baya ne aka gudanar da bikin wasanni a tsakanin matasan kasa da kasa karo na biyu, ciki hadda gasar wasan kwallon kafa ta sada zumunta ta kasa da kasa ta shekarar 2017 a birnin Meizhou na lardin Guangdong dake kasar Sin, inda dalibai daga kasashe da yankuna fiye da 30 suka halarci gasar. Haka zalika kuma, dalibai da masana masu kula da horar da 'yan wasa matasa a ciki da wajen kasar Sin, sun yi musayar ra'ayoyi, da more fasahohi, don neman wata hanyar bunkasa wasan kwallon kafa a tsakanin matasa a kasar Sin.

Kungiyoyi 8 sun halarci gasar a wannan karo, a cikinsu kungiyoyi uku na daliban kasashen waje ne dake karatu a Sin, daga jami'ar koyon harsunan waje da cinikayya ta Guangdong.

An ce, yanzu haka akwai dalibai daga kasashe fiye da 130 dake karatu a jami'ar koyon harsunan waje da cinikayya ta Guangdong. Kungiyar da ta samu nasara a gasar ta wannan karo kungiya ce ta hadin gwiwar daliban Asiya, da Afirka da Turai, wadda ta kunshe 'yan wasa 10 daga Indonesia, da Angola, da Mozambique, da Spaniya, da Koriya ta Kudu, kuma dukkansu ba masu cikakkiyar sana'ar wasan kwallon kafa ba ne.

Kyaftin din kungiyar shi ne Buekamba Benjamin Panzo wanda ya zo daga kasar Angola, ya bayyana cewa, ya kan buga kwallon kafa tare da abokansa tun na kuruciya. Bai kuma taba koyon fasahohin wasan kwallon kafa a jami'a ba. Ya ce, dalilai daga kasa da kasa dake karatu a jami'ar su, kan yi amfani da lokacin hutu don yin wasan kwallon kafa tare. Yace yana fatan amfani da tunanin wasan kwallon kafa don kyautata zaman rayuwar sa.

A shekarun baya baya nan, masu horaswa a fannin kwallon kafa daga kasashen waje masu kwarewa, na zuwa kasar Sin don horar da matasan kasar Sin a fannin wasan kwallon kafa.

Tsohon dan wasan kungiyar wasan kwallon kafa ta Portugal Andre Lima, wanda ya halarci gasanni 111 a matsayin memban kungiyar, ya fara horar da matasa wasan kwallon kafa a kasar Sin tun daga shekarar 2012. Game da muhimman fannonin dake shafar makomar wasan kwallon kafa ta matasa, Lima ya bayyana cewa, abu mafi muhimmanci shi ne hada tsarin bada ilmi da kasuwar wasan kwallon kafa tare. Domin a cewar sa yanzu lokaci ne na karatu tsakanin yara, kuma ya kamata a rika shirya kos na wasan kwallon kafa a makarantu.

Ya ce idan masu horaswa kamar shi suka samu damar horar da matasa a makaranta, hakan zai baiwa malamai a makarantu dama ta koyon fasahohin wasan, ta haka kuma za su iya kara koyar da fasahohin ga yaran dake makarantunsu.(Zainab Zhang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China