in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta Sin ta bayyana wasu ma'aikatan gwamnati dake tsere a ketare
2017-04-27 20:47:53 cri
A yau Alhamis ne, ofishin da ke farautar ma'aikatan gwamnatin da suka gudu zuwa kasashen ketare na hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta kwamitin tsakiyar kasar Sin ya bayar da wata sanarwa, inda aka bayyana wasu ma'aikatan gwamnatin da ke boye a ketare, wannan ne karo na farko da kasar Sin ta samar da bayanan wasu daga cikin ma'aikatan gwamnati guda 100 da suka gudu zuwa ketare wadanda kuma ake nemansu ruwa a jallo, ofishin yana fatan jama'ar kasar, da Sinawa dake kasashen ketare, da kuma abokai na kasashen ketare za su taimaka wajen ba da rahoto game da ma'aikatan. Ya kuma yi kira ga kasashen da batun ya shafa da su nuna goyon baya ga ayyukan yaki da cin hanci da rashawa na Sin, kana ya gargadi ma'aikatan da suka tsere, da su koma kasar Sin cikin sauri don su amsa laifinsu da kansu.

Ya zuwa ranar 31 ga watan Maris na bana, kasar Sin ta kama ma'aikata 2873 da suka gudu zuwa ketare tare da maido da kudaden da suka kai RMB biliyan 8.99. Amma duk da haka, akwai babban aiki a wannan fannin. Kididdiga na nuna cewa, ya zuwa ranar 31 ga watan Maris na shekarar 2017, akwai ma'aikatan gwamnatin kasar 365 da ake zargin sun aikata laifukkan cin hanci da rashawa, wadanda suka gudu zuwa ketare, kana da wasu 581 da ba a san inda suke ba. (Bilkisu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China