in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Firaministar Birtaniya na neman hadin kan kaso mai yawa na 'yan majalissar dokoki
2017-04-28 10:12:14 cri
Firaministar Birtaniya Theresa May, ta ce tana bukatar goyon bayan kaso mai tsoka na 'yan majalissun dokokin kasar, a gabar da kasar ke fuskantar karin kalubale, a shirin ta na ficewa daga kungiyar tarayyar Turai ta EU.

Theresa May ta bayyana hakan ne a jiya, yayin wani gangamin yakin neman zabe da ya gudana a birnin Leeds na jihar Yorkshire.

May dai na mai da martini ne game da wasu kalamai da shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta yi, cewa ficewar Birtaniya daga kungiyar EU ba abu ne mai sauki ba. Merkel wadda ke jawabi ga zauren 'yan majalissar wakilan kasar ta, ta ce alakar Birtaniya da EU za ta banbanta matuka. Domin kuwa a cewar ta Birtaniyar za ta zamo kasa mai matsayin bangare na 3, kuma ba za ta yi daidai da sauran kasashen dake kungiyar ta EU ba.

Game da hakan, Theresa May ta bayyanawa magoya bayan jami'iyyar ta cewa, kalaman dake fitowa daga mambobin EU a yanzu, na nuna hali na rashin tabbas da za a iya fuskanta, da wahalhalu, wadanda za su gadarwa tattalin arzikin kasar tarin matsaloli.

Wasu daga kalubalen da za a iya fuskanta dai a cewar ta, sun hada da hauhawar haraji, da karancin guraben ayyukan yi, da kuma karuwar bashi. Ta ce don haka ya zama wajibi, a samu kwararru dake da fahimtar makamar aiki, wadanda za su shige gaba. Kuma hakan na nuna cewa, babban zaben kasar dake tafe, zai kasance mafi mufimmanci a tarihin Birtaniya.(Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China