in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Najeriya: Akwai karancin na'urori na karfafa harkokin sadarwar zamani
2017-04-28 10:47:57 cri
Shugaban hukumar dake sa ido kan kamfanonin sadarwa a Najeriya NCC farfesa Umar Dambatta, ya ce na'urorin sadarwa da kasar ke da su, ba za su isa bukatun 'yan kasar ba. A daya hannun kuma akwai bukatar kafa sabbin cibiyoyi da na'urori na zamani, idan har ana fatan cin gajiya daga hidimomin fasahar sadarwa dake akwai a kasashen da suka ci gaba.

Da yake tsokaci yayin wani taron masu ruwa da tsaki game da harkokin sadarwa a jihar Legas dake kudancin Najeriya a jiya Alhamis, farfesa Dambatta ya ce a yanzu haka, Najeriyar na da cibiyoyin turakun sadarwa 50,000 ne, kasa da 80,000 da kasar ke bukata.

Ya ce samar da isassun irin wadannan cibiyoyi, zai baiwa kasar damar shiga jerin kasashe da ke cin cikakkiyar gajiya daga hidimomin sadarwa da ake wa lakabi da (IoT).

Jami'in ya kara da cewa, tsarin samar da hidimomin fasahar sadarwa na IoT, na share fagen cin gajiya daga sadarwar yanar gizo mai karfin 4G da 5G.(Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China