in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin tana fatan taron da kwamitin sulhu ya kira game da batun nukuliyar kasar Koriya zai aike da sakon da ya dace
2017-04-28 19:32:07 cri
Kasar Sin tana fatan taron ministocin da kwamitin sulhu yake gudanar a halin yanzu game da batun nukiliyar kasar Koriya ta arewa zai aike da sako mai gamsarwa ga duniya baki daya.

Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Geng Shuang wanda ya bayyana hakan yau yayin taron manema labarai da aka saba gudanarwa, ya ce idan taron ya mayar da hankali kan batun sanyawa kasar takunkumi da matsa mata lamba kadai, hakika bai yi amfani da kyakkyawar damar da ya samu ba, kuma hakan ka iya haifar ta yin fito na fito tsakanin bangarorin da abin ya shafa, da lalata kokarin da ake na yin tattaunawa.

Geng ya ce, kasar Sin a shirye ta ke ta shiga tattaunawar tare da musayar ra'ayoyi don neman hanyoyin warware wannan matsala.

Mahalarta taron sun hada da ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi, da sakataren harkokin wajen kasar Amurka Rex Tillerson da kuma babban sakataren MDD Antonio Guterres.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China