in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An shirya gagarumin bikin aza harsashi ga ginin da kasar Sin ke taimaka ginawa a kasar Liberiya
2017-04-28 20:18:55 cri
Gwamnatin kasar Liberiya ta shirya wani gagarumin biki a Monrovia, babban birnin kasar don nuna yabo da godiya ga gwamnatin kasar Sin don fara gina rukunin gine-ginen ma'aikatu da na majalisar dokokin kasar

Bayanai na nuna cewa, ayyukan za su lashe kimanin dala miliyan 60, Idan aka kammala su, gine--gine guda biyu za su kunshi ofisoshi da dakunan taro, babban zauren gudanar da taro, shagunan zamani da na adana kayan tarihi da dakin cin abinci. Sauran sun hada da kayayyakin alatu kamar fanfunan ruwa,na'urar samar da wutar lantarki da dakin injin janareta da sauransu.

A daya hannun kuma rukunin ginin ma'aikatun mai fadin sq mita 24,000, an tsara shi ne ta yadda kowa ce ma'aikata da hukumomin gwamnati za su samu ofishi a cikinsa, baya ga wasu mutane 1,300 da ginin zai iya dauka.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China