in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
'Yar jarida ta Tarayyar Najeriya Bukola Ogunsina
2017-06-13 10:17:15 cri

A ranar 1 ga watan jiya ne aka bude taro na 4, na ilmantar da 'yan jaridun nahiyar Afirka, game da muhimman batutuwa da suka shafi kasar Sin, da ma yanayin da ake ciki game da alakar kasar da nahiyar Afirka, a wani mataki na fadada musaya tsakanin Sin da nahiyar ta Afirka ta fannin watsa labarai. Kaza lika taron zai baiwa 'yan jaridu daga nahiyar ta Afirka damar ganewa idanun su, irin ci gaban da kasar Sin ta samu a fannonin siyasa, da raya al'adu da kuma inganta rayuwar al'umma da dai sauran sassan na ci gaba, a shirin da aka yiwa lakabi da CAPC.

Wannan dai bangare ne cikin jerin shirye shirye da kungiyar bunkasa diflomisiyya ta kasar Sin CPDA ke gabatarwa, a kuwa wannan karo shirin ya samu halartar 'yan jaridu 29 daga sassan nahiyar Afirka daban daban.

Bisa manufar shirin a cewar mashiryan sa, 'yan jaridun dake halartar sa za su samu zarafi na zagaya sassan kasar Sin, da cibiyoyin watsa labaran kasar daban daban, da masana'antu, su kuma samu zarafin musayar fahimta tsakanin su da masana a fannoni masu yawa.

A wannan gaba da aka fara gudanar da wannan shiri na bana, mun samu zantawa da daya daga 'yan jaridun dake halartar sa daga Najeriya, mai suna Bukola Ogunsina, ma'aikaciya a jaridar Leadership mai hedkwata a birnin Abuja fadar mulkin Najeriya.(Kande Gao)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China