in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Yawan irin miyagun kwayoyi ya karu sosai
2017-06-23 13:30:39 cri

A jiya ne ofishin yaki da miyagun kwayoyi da aikata laifuffuka na MDD ya gabatar da rahoton sa na shekarar 2017 game da illar miyagun kwayoyi a duniya,wanda ya yi bayani game da yadda ake cinikayyar miyagun kwayoyi a duniya a shekarar 2015. Rahoton ya bayyana cewa, a halin yanzu a fadin duniya, yawan nau'in miyagun kwayoyi ya karu sosai, tasirin da miyagun kwayoyi suka haddasa wa mutane ya yi tsanani sosai.

Rahoton da aka gabatar ya nuna cewa, mutane kimanin miliyan 250 a duniya sun taba yin amfani da miyagun kwayoyi a kalla sau daya a shekarar 2015, wanda ya kai kashi 5 cikin dari na yawan balagai a duniya, kana miliyan 29 da dubu 500 daga cikinsu sun kamu da cututtuka a sakamakon shan miyagun kwayoyi, yayin da wasu kuma suka kasa daina ta'ammali da miyagun kwayoyi. A cikin shekaru 10 da suka gabata, yawan mutanen da suka kamu da cututtuka ko suka mutu a sakamakon shan miyagun kwayoyi ya karu sosai.

Rahoton ya yi nuni da cewa, shan miyagun kwayoyi ta hanyar yin allura ya fi hadari. A cikin masu shan miyagun kwayoyi ta hanyar yin allura a duniya, kashi daya cikin kashi takwas suna dauke da cutar kanjamau, fiye da rabi na wannan adadi sun kamu da cutar gyambon hanta nau'in na uku(C). Kana masu shan miyagun kwayoyi sun fi fuskantar hadarin kamu wa da cutar tarin fuka.

Game da mata masu shan miyagun kwayoyi kuwa, ko da yake yawan maza masu shan miyagun kwayoyi ya ninka na mata sau biyu, amma idan mata suka fara shan miyagun kwayoyi, sun fi maza yawan sayan miyagun kwayoyi, kana sun fi maza fuskantar hadarin kamuwa da cututtuka a sakamakon shan miyagun kwayoyi.

Rahoton ya yi nuni da cewa, hodar iblis ta Opion ta fi kawo illa ga masu shan miyagun kwayoyi, wannan illa ta shafi yawan mutane da ya kai kashi 70 cikin dari na masu ta'ammali da miyagun kwayoyi, haka kuma ana iya fuskantar hadarin kamuwa da cutar kanjamau ko gyambon hanta na nau'in C ta hanyar yin allura.

Rahoton ya bayyana cewa, a shekarun baya baya nan, yawan na'uin miyagun kwayoyi da suka shiga kasuwa ya karu sosai, haka kuma ba a kawar da miyagun kwayoyi na gargajiya ba, kana ana bullo da sabbin miyagun kwayoyi a kowace shekara. Kana yawan tabar wiwi da aka samar ya kara karuwa, yawansu da aka samar a shekarar 2016 ya karu da kashi 1 cikin 3 bisa na shekara da ta gabata.

Kana kungiyoyin masu fataucin miyagun kwayoyi da aikata laifuffuka sun canja tsarin ayyukansu. A halin yanzu, kungiyoyin ba aikin sayar da miyagun kwayoyi kawai suke yi ba, har ma suna gudanar da wasu ayyuka kamar sayar da kayayyakin jabu, sace mutane, yin safarar mutane, sayar da makamai da dai sauransu.

Hakazalika kuma, fasahohin sadarwa na zamani sun bullo da wata sabuwar dama ga masu sayar da miyagun kwayoyi. Inda masu sayar da miyagun kwayoyi yanzu ba su bukatar gamuwa da masu sayen miyagun kwayoyi, maimakon haka suna amfani da internet wajen tura sako cikin sirri, da gaya wa masu sayen miyagun kwayoyi wurin da za su samu miyagun kwayoyin nasu.

Rahoton ya jaddada cewa, ya kamata kasa da kasa su tattara muhimman bayanai da nazarin yadda za a warware sabbin matsaloli yayin da suke magance batun miyagun kwayoyi. Sa kaimi ga samun bunkasuwa mai dorewa wata hanya ce ta taimakawa manoma su yi watsi da noman miyagun kwayoyi. Kana rahoton ya bada shawara ga kasa da kasa da su shigar da ma'aunin bada jinya ga masu shan miyagun kwayoyi da ofishin kula da miyagun kwayoyi da aikata laifuffuka na MDD da hukumar kiwon lafiya ta duniya suka tsara a cikin tsarin kiwon lafiyarsu. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China