in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mutane 3 sun mutu a jirgin ruwa da ya nutse a Colombia
2017-06-26 10:42:06 cri

A kalla mutane 3 ne suka mutu, sannan wasu mutane 30 suka bace a lokacin da wani jirgin ruwa mai dauke da fasinjoji 150 dake yin shawagi a wani tafki ya nutse da yammacin ranar Lahadi a arewa maso yammacin kasar Colombia, in ji wasu kafafen yada labaran yankin.

Babban jami'in 'yan sandan na sashen Antioquia a arewa maso yammacin Colombian ya fada a lokacin afkuwar lamarin a tafkin Penol-Guatape cewa, mutanen 3 sun mutu ne, kana wasu mutane 30 suka bace a sanadiyyar nutsewar jirgin ruwa

Victoria Eugenia Ramirez, sakataren gwamnatin Antioquia ya shedawa manema labarai cewa, tuni aka ankarar da jami'an sojin Colombia game da afkuwar lamarin.

Ramirez ya kara da cewa, suna gudanar da cikakken aiki a halin yanzu. A cewar kamfanin, mutane 150 ne ke cikin jirgin ruwan. Kana akwai jami'an aikin ceto da suka hada da na ma'aikatar cikin gida, da sojojin sama da 'yan sanda. Ya ce, jirgin mai suna 'El Almirante' (The Admiral) ba karo ya yi da wani jirgin ba, kawai dai ya nutse ne a cikin ruwa.

Jirgin dai na dauke ne da masu ziyarar rangadi a cikin tafkin mai nisan kilomita 80 daga gabashin Medellin, a lokacin da ya fara tangal-tangal, daga bisani kuma sai na nutse.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China