A wannan rana, babbar kotun Amurkar ta bayyana a wata takardar doka cewa, ta amince da yanke hukunci kan ko umurnin kayyaden baki da za su kaura daga ketare ya dace da doka ko a'a, kuma ya amince da sassauta hukunci da kotun tarayyar kasar Amurkar ta yanke na daskarar da wasu jimlolin umurnin nan take.
Bisa wannan takardar doka, umurnin ba zai kayyade wadanda ke da ainihin alaka da mutane ko kungiyoyi a Amurka wajen shiga kasar ba, yayin da zai kayyade wadanda ba su taba zuwa Amurka ba kuma ba su da dangi da sauran wata alaka da kasar wajen shiga kasar ta Amurka.
Ko da yake wannan takarda ta bayyana ra'ayin babbar kotun Amurka, amma ba tare da sa hannun manyan alkalai ba. Bisa labarin da kafofin yada labarai na Amurka suka bayar, an ce, a kalla manyan alkalai uku sun nuna rashin amincewa kan batun, a ganinsu, kamata ya yi a sassauta daskarar umurnin duka. (Fatima)