in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Jami'in MDD ya bukaci kasashen Afrika su yi rigakafin tashe tashen hankula
2017-06-27 14:06:16 cri

Wakilin musamman na MDD mai kula da rigakafin kisan kare dangi ya bukaci kasashen nahiyar Afrika su guji yin shugabanci na rashin adalci da aikata rashawa wadanda su ne ke haddasa yawaitar tashe tashen hankula dake sanadiyyar hasarar rayukan jama'a.

Tabbatar da kare bazuwar rikici da tashin hankalin da masu dauke da makamai ke haddasawa hakki ne da ya rataya a wuyan kasashen, har ma da masu ruwa da tsaki dake wajen kasashen, kana har ma da daidaikun jama'a, Adama Dieng ya bayyana hakan ne a lokacin taron shiyya game da kalubalolin da al'umma ke fuskanta a sakamakon ayyukan masu dauke da makamai a biranen duniya baki daya, wanda aka gudanar a Kigali, babban birnin kasar Ruwanda.

Dieng ya fada a lokacin taron cewa, akwai bukatar shawo kan matsalar rashawa a tsakanin gwamnatoci, ya ce dole ne a dauki wannan batu a matsayin al'amari mafi girma, ya ce ya kamata a yi la'akari da wannan batu sakamakon yadda yake hana ci gaba, kuma a mayar da hankali wajen ci gaban gwamnatoci da tsarin mulki na demokaradiyya

Ya kara da cewa, ba za ka taba samar da zaman lafiya da kwanciyar hankali ba matukar ba'a nazarci batun samar da ci gaba ba, kasancewa suna tafiya ne kafada da kafada. Ya ce, matsalar rikicin masu dauke da makamai ba zai zo karshe ba muddin shugabannin Afrika ba su zamanto masu gaskiya da yin aikin tukuru ba.

Hukumar ba da agaji ta Red Cross (ICRC), ita ce ta shirya wannan taron domin tattauna irin kalubalolin dake addabar ci gaban bil adama da karuwar tashe tashen hankula da masu dauke da makamai ke haddasawa a biranen duniya.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China