in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An fara taron WHO na Afirka na farko
2017-06-27 18:53:58 cri
A yau Talata ne hukumar lafiya ta duniya WHO ta bude wani dandalin kiwon game da Afirka na farko, (WHO AFRO) taron da ake fatan zai mayar da hankali wajen zakulo muhimman fannonin kiwon lafiya da kalubalen da harkar kiwon lafiya ke fuskanta da kuma hanyoyin inganta kiwon lafiya ga kowa da kowa.

Ofishin WHO mai kula da shiyar Afirka ne ya shirya taron na kwanaki biyu, bisa taken, "ba da muhimmanci ga jama'a: Taswirar inganta harkokin kiwon lafiya a nahiyar Afirka".

Bugu da kari, ana fatan taron zai bullo da sabbin matakan hadin gwiwa kan yadda za a samar da kiwon lafiya ga jama'a, da yadda jama'a za su samu kulawar lafiya cikin rahusa.

A jawabinta na bude taron Darektan ofishin WHO mai kula da shiyyar Afirka Matshidiso Moeti ta ce taron wani muhimman mataki ne na ci gaban da ake samu a fannin hadin gwiwar masu ruwa da tsaki, da nufin ciyar da ajendar kiwo lafiyar nahiyar gaba.

Ana saran gudanar da jerin shirye-shirye da suka shafi daukar nauyin harkokin kiwon lafiya, tsaron kiwon lafiyar kasa da kasa, bincike da yayata batutuwan da suka shafi kiwon lafiya da sauransu.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China