in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban kasar Sin zai ziyarci kasashen Rasha, Jamus tare da halartar taron G20
2017-06-27 19:17:35 cri
Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Lu Kang ya shaidawa taron manema labarai a yau Talata cewa, shugaba Xi Jinping na kasar Sin zai kai ziyarar aiki kasashen Rasha da Jamus daga 3 zuwa 6 ga watan Yuli.

Lu Kang ya ce shugaba Xi zai kai ziyara wadannan kasashen ne bisa gayyatar takwarorinsa na kasashen Rasha Vladimir Putin da na Jamus Frank-Walter Steinmeier da kuma shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel.

Ana kuma saran shugaba Xi zai halarci taron kolin kasashen kungiyar G20 da zai gudana a birnin Hamburg na kasar Jamus daga ranar 7 zuwa 8 ga watan Yuli. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China