in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shekaru ashirin da dawowar yankin Hong Kong bangaren kasar Sin
2017-07-13 15:16:09 cri

A ranar 1 ga watan Yulin shekarar 2017 ne, aka yi bikin cika shekaru 20 da yankin Hong Kong ya dawo bangaren kasar Sin daga hannun Burtaniya. Yankin Hong Kong dai yana daga cikin yankunan musamman na kasar Sin da suka hada da Taiwan da Macao.

Fadin yankin Hong Kong mai bin tsarin "kasa daya, tsarin mulki biyu", ya kai sq kilomita sama da dubu biyu. Kana yawan al'ummar yankin ya kai sama da miliyan bakwai.

A jawabinsa na bikin cikar yankin shekaru ashirin da dawowarsa bangaren kasar Sin, shugaba Xi Jinping na kasar Sin ya ce gwamnatin tsakiya za ta ci gaba da tallafawa yankin a fannin bunkasa tattalin arziki da zamantakewar al'ummarsa.

Shugaba Xi ya ce tsarin "kasa daya tsarin mulki biyu" shi ya fi dacewa da yankin wajen ci gaba da wanzar da zaman lafiya da makoma mai kyau, duba da irin ci gaba da yankin ya samu tun dawowarsa hannun kasar Sin a shekarar 1997. Don haka, dole ne a tsaya ga bin wannan tsari.

Masu fashin baki na cewa, yankin Hong Kong ya taka muhimmiyar rawa ga ci gaban tattalin arzikin kasar Sin da ma duniya baki daya. (Ahmed, Saminu, Ibrahim/Sanusi chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China