Mai martaba sarkin Kano na son karfafa hadin-gwiwa da kamfanonin kasar Sin a fannonion saka tufafi da mulmula karafa 2017-08-15 Jiya Litinin ne, mai martaba sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, ya ci gaba da ziyarar aikin da yake yi a birnin Shanghai dake gabashin kasar Sin, inda ya gana da manyan jami'an wasu kamfanonin kasar Sin guda biyu, wato kamfanin saka tufafi na Shangtex gami da kamfanin mulmula karafa mai suna Baowu. Mai martaba sarkin ya bayyana niyyarsa, ta habaka hadin-gwiwa da wadannan kamfanoni, tare da yin kira a gare su don su zuba jari a Najeriya, musamman a fannonin da suka shafi tufafi, wutar lantarki, ma'adinai da sauransu, don taimakawa rayuwar al'umma da raya tattalin arzikin tarayyar Najeriya.
|