Mai martaba sarkin Kano ya kai ziyara ofishin kungiyar bunkasa kasuwanci tsakanin Sin da Afirka
Kafin ya kammala ziyarar aikinsa kasar Sin, mai martaba sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, tare da 'yan tawagarsa sun ziyarci ofishin bunkasa harkokin kasuwanci tsakanin Sin da Afirka a yau Alhamis da yamma, inda mai martaba sarkin ya yi shawarwari tare da shugabannin kamfanoni kanana da matsakaita, da wasu 'yan kasuwan kasar Sin, wadanda ke da sha'awa ko niyyar zuba jari a Najeriya.(Murtala Zhang)