in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Harin da aka kai a birnin Barcelona na Spaniya ya haddasa rasuwar mutane 13
2017-08-18 09:39:35 cri

A jiya ne gwamnatin yankin Catalonia mai cin gashin kansa ta tabbatar da cewa, an kai harin ta'addanci a birnin Barcelona na kasar Spaniya, harin da ya haddasa rasuwar mutane guda 13, yayin da mutane 80 suka jikkata, kuma mutane guda 15 daga cikinsu sun ji rauni mai tsanani.

A yammacin jiya Alhamis ne, wata babbar motar dakon kayayyaki ta abkawa taron mutanen dake kan titin Las Ramblas a tsakiyar birnin Barcelona ba zato ba tsammani. Daga bisani rundunar 'yan sandan wurin ta sanar da cewa, binciken da suka gudanar ya nuna cewa, hadari ne na ta'addanci, kuma za a ci gaba da yin bincike kan lamarin

Bugu da kari, shugaban gwamnatin yankin Catalonia mai cin gashin kansa Carles Puigdmeont ya bayyana cewa, 'yan sanda sun kama mutane guda biyu, wadanda ake zargi suna da hannu a harin.

A jiya kuma, wata mota ta ki tsayawa lokacin da 'yan sanda guda biyu suka dakatar da ita a wata tashar binciken ababan hawa, amma daga bisani, an kama direban motar a birnin Barcelona, amma, 'yan sanda ba su tabbatar ko motar tana da alaka da harin da ya auku a birnin ba.

Firaministan kasar Spaniya Mariano Rajoy da sarkin kasar sun yi allah wadai da hare-haren da aka kai a kasar, inda suka bayyana cewa, 'yan ta'adda ba za su samu mafakar halaka al'ummomin kasar mai kaunar 'yanci da hadin kai ba.

A wannan rana kuma, kungiyar IS ta sanar da daukar alhakin kai wannan harin na birnin Barcelona. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China