in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sarkin Sifaniya ya halarci addu'o'i ga wadanda hare-haren kasar sa suka rutsa da su
2017-08-21 11:03:24 cri

Sarki Felipe VI na kasar Sifaniya da mai dakin sa Letizia, sun halarci addu'o'in da aka gudanar ga wadanda suka rasa rayukan su, sakamakon hare-haren da aka kaddamar a birnin Barcelona da Cambrils, da sanyin safiyar ranar Lahadi a wani gini dake Sagrada Familia. Mutane 14 ne dai suka rasa rayukan su yayin tagwayen hare-haren, ciki hadda 'yan kasar Portugal biyu.

Taron dai ya samu halartar manyan jami'an gwamnatoci da suka hada da firaministan Sifaniya Mariano Rajoy, da mataimakiyar sa Soraya Saenz de Santamaria, da mai rikon mukamin magajin birnin Barcelona uwar gida Ada Colou da jagoran yankin Catalan Carles Puigedemont.

Kaza lika firaministan kasar Portugal Antonio Costa, da shugaban kasar Marcelo Rebollo de Sousa, sun halarci addu'o'in, domin martabawa ga 'yan kasar su da wannan lamari ya rutsa da su. Har wa yau wasu wakilai daga hukumomi da sassan jami'an tsaro su ma sun halarci addu'o'in.

A hannu guda, daruruwan fararen hula 'yan kasar, da ma baki 'yan yawon bude ido sun nuna goyon bayan su ga taron na Barcelona.

A wani ci gaban kuma, mahukuntan birnin Barcelona da na Catalan sun sanar da shirin su na gudanar da wani gangami, wanda za a gudanar a ranar 26 ga watan nan na Agustan a wasu tituna dake birnin Barcelona, domin nuna adawa da ayyukan ta'addanci.(Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China