in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ya kamata Japan ta nuna da gaske take yi wajen inganta hulda da Sin
2017-08-22 19:40:50 cri

Kasar Sin ta bukaci kasar Japan da ta nuna lallai da gaske take yi wajen inganta huldar da kasar Sin. Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Madam Hua Chunying wadda ta bayyana hakan a yau Talata, biyo bayan rahotanni da ake nuna cewa, ministan harkokin wajen Japan Taro Kono yana shirin kai ziyara nahiyar Afirka a gobe Laraba domin halartar taron kolin kasa da kasa na ministocin Tokyo game da raya nahiyar Afirka(TICAD), inda zai gabatar da kiran 'yancin yin zirga-zirga a tekun kudancin kasar Sin.

Madam Hua ta ce, kamata ya yi taron na TICAD ya mayar da hankali wajen samar da zaman lafiya da ci gaban nahiyar Afirka.

Jami'ar ta Sin ta ce, a halin yanzu an samu ingantuwar al'amura a yankin tekun kudancin kasar Sin, sakamakon hadin kai da kokarin kasar Sin da kasashen yankin ASEAN.

Don haka Hua ta bukaci Japan da ta mutunta kokarin da kasashen dake shiyyar suke yi wajen tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a tekun kudancin na Sin.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China