in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin na fatan Indiya za ta nuna da gaske take yi kan batun yankin Dong Lang
2017-08-22 20:28:05 cri

A jiya Litinin ne, ministan harkokin cikin gidan kasar Indiya Rajnath Singh ya ce, nan ba da dadewa ba za a lalubo bakin zaren warware batun fito na fito da kasashen Indiya da Sin suke yi a yankin Dong Lang.

Dangane da kalaman ministan, yau Talata, madam Hua Chunying, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin ta bayyana a nan Beijing cewa, kasar Sin na fatan Indiya za ta nuna lallai da gaske take yi kan batun. Madam Hua ta kuma jaddada cewa, hanya daya tak da kuma sharadi guda wajen warware batun shi ne Indiya ta hanzarta janye dukkan mutanenta da na'urorinta da ke yankin kasar Sin ba bisa doka ba ba tare da gindaya wani sharadi ba. (Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China