Rahoton Sky News ya ruwaito cewa, mai shari'a Andreu ya yanke hukuncin ne bayan sauraron karar.
An tuhumi wadanda ake zargin 2 da suka hada da Chemlal da Driss Oukabir da kisan kai da zama 'ya'yan kungiyar ta'addanci da kuma mallakar ababen fashewa, inda za a rike su a gidan yari ba tare da beli ba.
Mutum na 3 da ake zargi kuwa, za a rike shi na tsawon sa'o'i 72 yayin da za a ci gaba da bincike kansa.
Shi kuwa na hudun, Mohammed Aalla, an sake shi bisa rashin kwararan shaidu da za su tabbatar da laifin da ya aikata.
Mutanen hudu daga cikin 12 da ake zargi da kai hare-hare cikin makon da ya gabata a Barcelona da Cambrils, sun bayyana ne gaba babbar kotun kasar Spaniya a jiya Talata. (Fa'iza Mustapha)