in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Jami'in MDD yana fata za'a warware rikicin Afghanistan ta hanyar siyasa
2017-08-23 12:28:11 cri
Biyowa bayan kalaman da shugaban Amurka Donald Trump yayi na tura karin dakaru zuwa kasar Afghanistan, sakatare janar na MDD Antonio Guterres ya sanar a jiya Talata cewa, yana fata za'a bi matakan siyasa wajen warware rikicin kasar ta Afghanistan.

Mai magana da yawun babban sakataren MDD Stephane Dujarric, ya ce mista Guterres abin da yake tunani shi ne, abu mafi muhimmanci shi ne, ya kamata kasashen duniya su hada kai don tallafawa kasar Afghanistan don ta lalibo hanyar warware rikicin kasar ta hanyar matakai na siyasa.

Amurka ta tura dakarunta kasar Afghanistan ne tun a shekarar 2001.

Trump ya bada sanarwa a ranar Litinin cewa ya yanke shawarar tura karin dakaru, saidai bai bayyana adadin da zai tura da kuma takamamman lokacin da zai tura karin dakarun ba, ko da yake a lokacin yakin neman zabensa, Trump ya sha nanata aniyar Amurkar na ficewa daga kasar Afghanistan. Wannan shine yaki mafi dadewa a tarihin Amurka.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China