in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Iraqi: MDD na tallafawa fararen hula dake ficewa daga Tal Afar
2017-08-23 13:35:47 cri
Wasu rahotanni daga Iraqi na cewa yanzu haka hukumar dake kula da kaurar jama'a ta MDD, na tallafawa fararen hula dake tserewa daga birnin Tal Afar da kayayyakin jin kai.

Dubban fafaren hula ne dai ke ficewa daga Tal Afar, birnin dake yamma da Mosul, tun bayan da dakarun sojin kasar suka fara kaddamar da hare hare kan mayakan IS dake tunga a cikin sa.

Birnin Tal Afar, na da nisan kilomita 70 daga Mosul, kuma shi ne birni na karshe dake hannun mayakan IS a daukacin lardin Nineveh, a arewacin kasar ta Iraqi. Kaza lika yana da yawan jama'a da suka kai mutum 350,000, mafi yawan su 'yan Sunni da mabiya akidar Shi'a, baya ga Kurdawa 'yan tsirarru.

Wata sanarwa da hukumar kula da masu kaura ta MDD IOM ta fitar ta bayyana cewa, mafi yawan fararen hula dake barin Tal Afar, na tafiyar kasa ta tsawon sa'o'i da dama, inda suke isa tudun mun tsira a galabaice, yayin da wasun su ke fama da matsananciyar yunwa da matsaloli na rashin lafiya musamman ma kananan yara. Sanarwar ta ce IOM da abokan huldar ta na cikin Iraqi, sun dukufa wajen samar da tallafin matsugunai, da kayan kula da lafiya ga al'ummun da suka tserewa yankuna da dama, musamman ma Tal Afar.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China