Wata sanarwa da mahukuntan Chadin suka fitar, ta ce daukar wannan mataki ya zama tilas, idan aka yi la'akari da illar da Qatar din ka iya yiwa Chadi idan har ba a gaggauta daukar matakai ba.
Kaza lika sanarwar ta ce nan da 'yan kwanaki, Chadi za ta rufe na ta ofishin jakadancin dake Qatar tare da maida ma'aikatan sa gida, duka dai da nufin wanzar da zaman lafiya da lumana a kasar da ma yankin da ta ke.
A watan Yunin da ya gabata ma dai kasashen Chadi, da Mauritania da Senegal sun bi sahun Saudiya da sauran kasashen larabawa, wajen janye jakadun su daga Qatar.
Hakan kuwa ya biyo bayan daukar makamancin wannan mataki ne da Saudiyya tare da wasu kawayen ta suka yi, inda kasashen suka katse huldar jakadanci da kasar ta Qatar tare kuma da rufe kan iyakokin su na sama, da kasa, da ruwa dake tsakanin su da kasar, tun daga ranar 5 ga watan Yunin da ya gabata.(Saminu Alhassan)