in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Masana sun bukaci a inganta hanyoyin samun taimakon shari'a ga masu rauni a Afrika
2017-08-24 09:50:24 cri
Masana harkokin shari’a, sun yi kira ga gwamnatocin Afrika su taimaka wajen saukaka hanyoyin shari’a ga masu rauni a fadin nahiyar. Masanan sun yi wannan kira ne a jiya, yayin taron yini 3 da aka fara ranar Talata, wanda na hadin gwiwa ne tsakanin bangaren shari’a na Gwmanati da cibiyoyin shari’a na al’umma, kan saukaka hanyoyin shari’a a Afrika, dake gudana a Kigali babban birnin kasar Rwanda. Taron na mai da hankali ne kan dabi’un dake tasiri kan harkokin shari’u, tun daga cikin al’umma har zuwa manyan kotuna, da nufin samar da fahimta da hadin giwa da kuma goyon baya. Bernardo Espanhola, Alkalin al’umma a Maputo na kasar Mozambique, ya shaidawa mahalarta taron cewa, samun shari’a ga talakawa na da tsada, a don haka, akwai bukatar kafa asusun da zai rika kula da su. Taron ya samu mahalarta daga sama da kasashe 15 na ciki da wajen nahiyar. (Fa’iza Mustapha)
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China