in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
MDD ta bukaci Amurka da ta kyamaci wariyar launin fata
2017-08-24 09:51:16 cri
Kwamitin MDD mai rajin yaki da nuna wariyar launin fata ko CERD a takaice, ya yi kira ga mahukuntan kasar Amurka, da su fito fili karara, su soki manufofi masu yayata akidar nuna wariyar launin fata, da sauran laifuka da aka aikata a garin Charlottesville, da ma sauran wasu yankuna dake kasar.

Wata sanarwa da kwamitin ya fitar ta bayyana cewa, babu wata mafaka ga masu nuna wariyar launin fata, ko masu fifita fararen fata sama da sauran mutane, domin hakan ya sabawa akidar mutunta bil Adama, da wanzar da daidaito.

Baya ga bincikar batun kutsa kai da mota cikin masu zanga zangar lumana da wani mutum ya aikata a birnin na Charlottesville, a hannu guda kwamitin na MDD, ya ja hankalin Amurka, da ta dukufa wajen lalubo tushen yaduwar irin wannan mummunar akida ta kin jinin wani jinsi.

A ranar 12 ga watan Agustan nan ne dai masu rajin martaba fararen fata, da 'yan ra'ayin rikau fararen fata, suka yi taho mu gama da masu adawa da su, yayin wata zanga zanga da ta gudana a Charlottesville, garin da shi ne mahaifar Thomas Jefferson, lamarin da ya sabbaba kisan mutane da dama tare da jikkatar wasu.

Shugaba Donald Trump na Amurka dai ya yi Allah wadai da aukuwar tarzomar, to sai dai kuma bai fito fili ya soki masu ra'ayin nuna wariya ba.(Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China