Sanarwar da AU ta fitar tace, shugabar sashen walwalar jama'a ta kungiyar Amira Elfadil, ta isa birnin Freetown ne tun a ranar Talata, domin bayyana goyon bayan AU da kuma tallafawa gwamnatin Saliyo sakamakon ibtila'in da ya afku.
AU zata mika cakin kudi na dalar Amurka dubu 100 a matsayin wani bangare na gudumowar da AU ta baiwa gwamnatin Saliyo, sakamakon ibtila'in zaftarewar laka, wanda yayi sanadiyyar hallaka akalla mutane 500, kana wasu sama da 600 suka bace, sannan wasu dubban mutane suka rasa matsugunansu.
Bugu da kari, a wata sanarwar ta daban, shugaban na AU ya mika sakon ta'aziyyarsa ga gwamnatin Guinea da ta jamhuriyar demokaradiyyar Congo DRC, sakamakon bala'in tsagewar kasa da aka samu a kasashen wanda ruwan sama ya haddasa.
A kalla mutane 8 ne suka hallaka a gundumar Ratoma dake wajen birnin Conakry hedkwatar mulkin kasar Guinean, yayin da mutane 200 kuma suka rasa rayukansu a lardin Ituri dake arewa maso gabashin DRC.
Shugaban kungiyar AU Moussa Faki Mahamat, ya jaddada aniyar AU wajen tallafawa kasashen nahiyar Afrika don daukar kwararan matakai na tunkarar afkuwar bala'o'i.