in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Nasarorin BRICS cikin shekaru goma
2017-09-14 13:26:50 cri

A shekarar 2001 ne, Jim O'Neill, babban masani kan tattalin arziki dake aiki a kamfanin Goldmansachs na Amurka ya fara tunanin wannan ra'ayi na "Kasashen BRICS" a karo na farko a duniya. A watan Yuni na shekarar 2009, shugabannin kasashen BRICS suka yi ganawar farko a hukunce a kasar Rasha. Daga bisani, a watan Disamba na shekarar 2010, kasashen na BRICS suka cimma matsaya daya wajen shigar da kasar Afirka ta Kudu cikin kungiyar.

Daga bisani shugabannin kungiyar kasashen (BRICS) da suka hada da kasashen Brazil, Rasha, India, Sin da kuma Afirka ta Kudu, yayin taron kungiyar karo na 6 a Fortaleza na Brazil sun bayyana aniyarsu ta kafa wani bankin musamman na tsimi da samar da ci gaba.

Manufar kungiyar ta BRICS ta kafa bankin, wanda ya fara aiki da jarin dalar Amurka miliyan dubu 100, ita ce baiwa kasashe mabukata, musamman masu tasowa damar kaucewa fadawa matsalolin kudi da samar da rance domin rage kaifin matsalolin tattalin arziki. Har wa yau ana fatan wannan tsari zai taimaka wajen kara hada kan kasashe mambobin kungiyar tare da baiwa tsarin tattalin azikin duniya kariya ta musamman bisa tsare-tsaren da ake da su a halin yanzu.

Kana yayin taron kungiyar karo da 9 da ya gudana a Xiamen na kasar Sin, shugaba Xi Jinping ya bayyana kudurin kasarsa na samar da dala miliyan 500 ga bankin a matsayin kudin ajiya. Ya kuma bayyana cewa,baki daya shugabannin kasashen BRICS suna ganin cewa, zurfafa hadin a fanni harkokin siyasa da tsaro, da kara amincewa da juna bisa manyan tsare-tsare sun dace da muradun kasashen biyar kamar yadda sauran kasashen duniya ke fatan gani. Ya ce, suna goyon bayan ci gaba da sa kaimi ga ci gaban hadin gwiwa a fannin siyasa da tsaro,don taka rawar da ta dace, a fannin kiyaye zaman lafiya da tsaro a duniya baki daya.

Masana na ganin cewa, wannan manufa ta BRICS, za ta taimaka wajen daga matsayin kasashen kungiyar na yada manufofi da tunaninsu a harkokin duniya, baiwa kasashe masu tasowa ikon fadin albarkacin baki da kuma shimfida yanayi mai kyau ga tattalin arzikin duniya. (Saminu, Fa'iza, Ibrahim/Sanisi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China