in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
UNESCO na bakin cikin janyewar Amurka daga hukumar
2017-10-13 11:14:51 cri

Babbar Daraktar hukumar bunkasa ilimi, kimiyya da raya al'adu ta MDD UNESCO Irina Bokova, ta ce ta yi bakin ciki sosai da kudurin Amurka na janyewa daga hukumar, tana mai bayyana shi a matsayin hasara ga hadin gwiwar kasa da kasa.

Cikin wata sanarwa da Babbar Daraktar ta fitar game da kudurin na Amurka, ta ce akwai bukatar inganta aikin samar da ilmi da tattaunawa yayin da ake yaki da tsattsauran ra'ayi, amma abun bakin ciki ne yadda Amurka ta janye daga hukumar dake kula da aikin a wannan lokaci.

Ta kara da cewa, janyewar Amurka daga hukumar mai kula da inganta samar da ilmi da zaman lafiya da kuma kiyaye al'adu bai kyautu ba a wannan lokaci da ake fuskantar rikice-rikice a wurare daban-daban na duniya.

Baya ga haka, Irina Bokova ta nuna cewa, har yanzu hukumar ba ta kammala ayyukanta ba, kuma za ta ci gaba da kokarin kafa duniya mafi adalci da zaman lafiya da kuma daidaito a karni na 21, aikin da ke bukatar shigar dukkan kasashen duniya.

A cewar Irina Bokova, ko da yake kasar Amurka ta ki biyan kudinta na mamba tun daga shekarar 2011, ana kara zurfafa dangantaka tsakaninta da hukumar.

Ta ce ta yi imanin cewa, UNESCO na iya biyan bukatun jama'ar kasar Amurka a fannin yaki da jahilci da kara ingancin ilmi da hadin kai a fannin kimiya da fasaha da dai sauransu.

A shekarar 2011 ne babban taron UNESCO ya zartas da kuduri shigar da Falestinu cikin hukumar a matsayin mamba, al'amarin da ya sanya gwamnatin Amurka sanar da cewa, za ta dakatar da biya kudin mamba don mayar da martani kan batun. (Bilkisu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China