in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Za a ci gaba da tunawa da ziyarar shugaba Xi Jinping a asibitin sada zumunta na Sin da Congo Brazaville har abada
2017-10-16 11:13:04 cri
A yankin Mfilou dake yammacin karkarar Brazaville, hedkwatar Jamhuriyar Congo, akwai wani asibitin sada zumunta da kasar Sin ta gina, ta kuma bada shi kyauta ga Jamhuriyar Congo.

A ranar 30 ga watan Maris din shekarar 2013 ne shugaban kasar Sin Xi Jinping wanda ya ke ziyara a kasar ya halarci bikin kaddamar da asibitin tare da takwaransa Denis Sassou Nguesso.

Kamfanin gine-gine na kasar Sin ne ya gina wannan asibitin da gwamnatin kasar ta bada shi kyauta ga Jamhuriyar Congo, inda ta kashe CFA franc biliyan 5.6 wajen gina shi. Wannan asibiti ya mamaye gonaki fiye da murabba'in mita 6300, inda ke da gadaje dari 1. A yanzu haka, shi ne asibiti mafi girma a yankin Mfilou, inda mutane masu fama da talauci suka fi yawa. An kuma kyautata yanayin kiwon lafiya sosai a yankin tun bayan kaddamar da asibitin.

Bayan bikin kaddamarwar, shugaba Xi ya kuma gaida masu aikin jinya na kasar Sin dake aiki a asibitin, inda ya gabatar da wani muhimmin jawabi.

Shugaba Xi ya jaddada cewa, domin nuna soyayyarsu ga duk fadin duniya, a cikin shekaru 50 da suka gabata, tawagogin masu aikin jinya na kasar Sin sun kafa wani tarihi na shawo kan matsaloli a lokacin da suke kokarin bayar da gudummawa wajen ceton rayukan wadanda suka kamu da cututtuka,

Mr. Wang Zhiyong, shugaban tawagar masu aikin jinya ta kasar Sin wadda ke aiki a asibitin yanzu, ya ce masu aikin jinya na kasar Sin da aka tura yankuna daban-daban na duniya, sun sanya yabon da shugaba Xi Jinping ya yi musu a zukatansu. Yanzu haka, akwai masu aikin jinya 33 na kasar Sin wadanda ke aiki a asibitoci biyu na Jamhuriyar Congo.

Martine Beatrice Pongui, shugabar asibitin sada zumunta na Sin da Congo Brazaville, ita ma ta halarci bikin kaddamar da asibitin, inda ta ce, "Muna godiya ga kasar Sin. Shugaba Xi Jinping da shugabanmu Sassou Nguesso sun halarci bikin kaddamar da asibitinmu, wannan wani muhimmin lokaci ne ga hadin gwiwar kiwon lafiya da ke tsakanin kasashen biyu. Wannan ne asibiti na farko da shugaba Xi Jinping ya kaddamar da shi a Afirka tun bayan da ya hau kan mukamin shugabancin kasar Sin. Sabo da haka, muna alfahari da shi sosai. Yanzu, akwai wani asibitin sada zumunci da kasar Sin ta gina a kasarmu Congo Brazaville. A ganinmu, wannan asibiti na alamta zumuncin dake tsakanin kasashen Sin da Congo Brazaville."

Mr. Milandou Emmanuel, direkta mai kula da harkokin hadin gwiwa tsakanin kasa da kasa a ma'aikatar kiwon lafiya ta Jamhuriyar Congo shi ma ya halarci bikin. Inda ya bayyana cewa, "Shugaba Xi Jinping aminin al'ummar Congo ne, muna kaunar sa kwarai. Muna kuma jin dadi sosai domin Shugaba Xi ya halarci bikin kaddamar da asibitin da kansa. Ya bayar da babbar gudummawa ga al'ummomin Afirka."

Shi ma Mr. Mananga Eric wanda ke kula da harkokin yau da kullum da kwadago a asibitin, ya yabawa shugaba Xi Jinping, yana mai cewa, "A cikin zuciyarmu, shugaba Xi Jinping yana da kirki. Kasar Sin kuma wata babbar kasa ce. Yanzu tana kokarin kafawa ko bunkasa huldar diflomasiyya irin ta sada zumunci tsakaninta da kasashen Afirka, musamman tsakaninta da Jamhuriyar Congo. Shugaba Xi Jinping wani babban dan siyasa ne a karni na 21, tabbas al'ummar Afirka za su rika tunawa da shi a kullum. A karkashin jagorancinsa, kuma bisa huldar sada zumunta tsakanin kasashen Sin da Afirka, al'ummar Congo Brazaville suna fatan za a kara hadin gwiwa tsakanin kasashen biyu a fannonin kiwon lafiya da tarbiya. Sannan, shugaba Xi Jinping wani muhimmin shugaba ne da ake martabawa sosai. Ba za a iya kauracewa kasar Sin ba a duk lokacin da ake zantawa kan harkokin siyasar kasa da kasa a yau. Yanzu kasar Sin ta kasance cibiyar harkokin siysasa na kasa da kasa, ta kuma samar da dimbin taimako ga sauran kasashen da tattalin arzikinsu ke bunkasa cikin sauri da kuma kasashe masu tasowa. Sabo da haka, a matsayin shugaba mai martaba na karni na 21, muna son shugaba Xi Jinping sosai a cikin zukatanmu." (Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China