in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin ta kafa wani sabon bajinta a fannin noman shinkafa a duniya
2017-10-16 20:30:45 cri
Masanin tagwaita irin shinfaka na kasar Sin Yuan Longping, ya sake kafa wani sabon kambun bajinta na duniya a fannin tagwaita irin shimkafa.

Rahotanni na cewa, a yau ne hukumomin lardin Hebei dake arewacin kasar Sin suka bayyana cewa, tawagar tagwaita irin shimkafar da Yuan Longping ya jagoranta, ta cimma nasarar samun shimkafar da ta kai tan 17.2 a eka guda.

Masanin wanda aka fi sani da jagoran tagwaita irin shimfaka na kasar Sin, ya fara gudanar da bincike ne kimanin shekaru 50 da suka gabata, kuma tun wancan lokaci ya ke kafa sabbin kambun bajinta a wannan fanni.

Kimanin kashi 65 cikin 100 na al'ummar Sinawa dai sun dogara ne ga shinkafa a matsayin abincin yau da kullum.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China