in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Za'a fara aikin gina layin jirgin kasa mai saurin tafiya a yankin da zai karbi bakuncin gasar wasannin Olympics na lokacin hunturu a 2022
2017-11-29 09:47:09 cri
Nan gaba kadan za'a fara aikin gina layin jirgin kasa mai saurin tafiya a Zhangjiakou, birnin dake arewacin kasar Sin, wanda zasu karbi bakuncin gasar wasannin Olympics na lokacin hunturu a shekarar 2022 tare da hadin gwiwar birnin Beijing.

Tashar jirgin kasan ta kudancin Zhangjiakou tana lardin Hebei, zata dinga kammala aikinta ne a daren ranar Asabar bayan jirgin kasar na fasinja ya kammala jigilarsa. Daga nan sai ya canza zuwa tashar Shalingzi dake yammacin birnin.

Tashar ta kudancin Zhangjiakou ta gudanar da aikin jigilar fasinjoji sama da miliyan 20, tun daga lokacin data fara aiki a shekarar 1957. Tashar ba zata iya biyan muradun yawan fasinjojin dake karuwa a yankin a kullum ba.

Ana saran za'a kammala aikin layin jirgin kasan mai saurin tafiya mai nisan kilomita 174 daga Beijing zuwa Zhangjiakou nan da shekarar 2019, inda za'a rage tsawon lokacin da ake shafewa wajen zirga zirgar tsakanin biranen biyu daga awowi uku zuwa mintoci 50.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China