in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An shirya babban taron kiyaye muhalli na MDD mai taken 'kafa duniyar da babu gurbatar muhalli'
2017-12-05 14:27:37 cri

Jiya Litinin ne, aka bude babban taron kiyaye muhalli na MDD karo na 3 a hedkwatar shirin kare muhalli na MDD, wato UNEP a takaice da ke birnin Nairobin kasar Kenya. A yayin taron mai take 'kafa duniyar da babu gurbatar muhalli', za a mai da hankali kan batun gurbata muhalli, da kokarin cimma muhimman kudurori da dama, kana da yin kira ga kasashen duniya da su dauki matakan gaggawa da suka dace don tinkarar kalubalen muhalli.

Taron da ya hallara wasu jami'an gwamnati, masu masana'antu, shugabannin al'umma da suka fito daga kasashe daban daban, inda za su tattauna kan yadda za a tinkari kalubalen da gurbata muhalli ke haifarwa a fadin duniya. Alkaluman kididdiga na nuna cewa, yawan mutanen da suka halarci wannan taron na kwanaki 3, ya wuce dubu 4. A lokacin taron, matakan da wasu kamfanonin kasar Sin suke dauka na tinkarar matsalar gurbata muhalli na jawo hankulan jama'a sosai.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China