A wani kuduri da aka amince da shi a jiya, babban zauren MDD ya bukaci dukkan mambobin majalisar, su rika bikin ranar a kowacce shekara yadda ya kamata bisa muhimman batutuwan da suka shafesu, ta hanyar ilmantar da jama'a da gudanar da shirye-shirye, domin kara wayar da kai game da bukatar ingantaccen tsarin kiwon lafiya da zai isa ga kowa.
Zauren majalisar ya yi kira da a yi kokarin ganin dukkan mutane suna samun dama iri guda ta samun kiwon lafiya domin inganta matakan kariya da gyara da tunkarar cuttutuka dake kunshe cikin tsarin kiwon lafiya
Majalisar ta kuma yi kira da a kara kare lafiya da rayukan jami'an kiwon lafiya da masu aikin agajin jin kai, tare da kula da hanyoyin sumfurinsu da kayakin aiki da asibitoci, musammam a wuraren da ake rikici. (Fa'iza Mustapha)