in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Gwamnatin Syria da bangaren adawa na ci gaba da tattaunawar neman sulhu a Geneva
2017-12-13 10:31:47 cri
Ana ci gaba da tattaunawar neman sulhu tsakanin Gwamnatin Syria da bangaren dake adawa da ita, inda manzon musammam na MDD Staffan de Mistura ke tattaunawa da bangarorin a lokuta daban-daban.

Wannan shi ne zagaye na 8, na tattaunawar neman sulhu a Syria da MDD ke jagoranta.

Babu wani tsokaci da ya fito daga wakilan Gwamanti karkashin jagorancin wakilin kasar a MDD Bashar al Jaafari game da tattaunawar da suka yi da manzon na MDD. Sai dai, bangaren adawa sun yi ikirarin cewa, akwai wata dama a tattaunawar ta wannan mako, da ya zama dole su yi amfani da ita domin al'ummarsu.

Bangaren adawar dai, ya tsaya kai da fata kan matsayinsa dake neman sai shugaban kasar Bashar al-Assad ya sauka daga mulki, a matsayin sabon babi na tsarin siyasa, wanda kuma Gwamnati ke ganin ba mai yuwa ba ne, tun da dakarunta sun kwace iko da muhimman yankunan kasar daga hannun 'yan tawaye.

An shirya cewa, sabon zagayen tattaunawar neman zaman lafiya a Syria da MDD ke jagoranta da aka fara a ranar 28 ga watan Nuwamba, zai ci gaba da gudana har zuwa ranar 15 ga watan nan na Decemba. MDD ta bayyana rashin aminta da juna a matsayin babban tarnakin dake hana samun nasarar tattaunawar. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China