in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
'Yan kasashen Afrika a Afrika ta kudu sun yi zanga-zangar kyamar cinikin bayi
2017-12-13 10:32:31 cri
Dubun dubatar 'yan kasashen Afrika ne suka yi maci a birnin Tshwane dake babban birnin Afrika ta kudu a ranar Talata, inda suka yi tir da batun rahotannin dake nuna cewa ana cinikin bayi a kasar Libya.

Dandalin tattauna harkokin mazauna kasashen ketare (ADF) wanda ta kunshi mambobi daga kasashen Afrika 35 ita ce ta shirya zanga-zangar. Zanga zangar ta samu halartar kungiyoyin fararen hula, da na coci-coci, da kungiyar 'yan kasuwa, da kuma shugabannin al'umma. Da yake zantawa da kamfanin dillancin labarai na Xinhua a lokacin gangamin, Marc Gbaffou, shugaban dandalin tattauna harkokin mazauna kasashen ketare ya bayyana damuwa dangane da batun cinikin bayin.

Masu zanga zangar sun mika takardar kokensu ga ofishin shugaban kasar Afrika ta kudun, da ofishin jakadancin Libyan dake Afrika ta kudun, da kungiyar tarayyar Afrika, da majalisar gudanarwar kasashen Afrika, da MDD, da kuma kungiyar tarayyar turai. Gbaffou ya bayyana cewa, suna fatan Afrika ta kudun wacce keda karfin fada aji a nahiyar Afrika zata taimaka wajen kawo karshen batun cinikin bayin a Libya dama dukkan sassan duniya.

Yace suna fata kungiyar tarayyar Afrika AU, zata hanzarta yin bincike da kuma tabbbatar da hukunta wadanda keda hannun kan wannan mummunan laifi. Kana yace sun bukaci AU data hana sauran kasashe aikata cinikin bayin.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China