A cewar wani mazaunin yankin, an kaddamar da harin ne da misalin karfe 7 zuwa 8 na dare agogon yankin, wanda yayi dai dai karfe 8 zuwa 9 agogon GMT a ofishin 'yan sanda na Mayo-Sava dake garin Amchide, wanda ke makwabtaka da Najeriya.
Maharin bam din ya hallaka wani mutumin kauye, a lokacin da maharin yayi amfani da yanayi na duhun dare wajen kaddamar da harin a lokacin da mutane ke kokarin halartar salla.
Ofishin 'yan sanda na Mayo-Sava ya fuskanci hasarar rayuka har na mutane 6, wanda ke da nasaba da Boko Haram daga ranar Litinin.