in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sudan ta kudu ta tsaurara tsaro gabanin bukukuwan karshen shekara
2017-12-13 11:19:36 cri

Hukumar 'yan sandan kasar Sudan ta kudu (SSNPS), ta tsaurara matakan tsaro a dukkan yankunan kasar da ake fuskar barazanar tsaro gabanin gudanar da bukukuwan karshen shekara a kasar.
James Dak Carol, mataimakin kakakin hukumar 'yan sandan kasar, ya shedawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua cewa, an tura jami'an tsaro a dukkan muhimman yankunan kasar.

Dak yace, an tsaurara matakan tsaro a babban birnin kasar, da manyan garuruwa da kuma sauran yankunan kasar a matsayin wani shiri na rigakafin barkewar tashin hankali a kasar baki daya.

Yace domin samun zaman lafiya a Juba, babban birnin kasar, sun yi kyakkyawan tanadi inda aka kasa birnin na Juba zuwa shiyyoyi 5, kuma an tura jami'an tsaro masu yawa a yankunan domin tabbatar da kare lafiyar al'ummar kasar a lokutan bukukuwan kirsimeti dana sabuwar shekara.

Mataimakin kakakin 'yan sandan ya ce za'a gudanar da aikin tabbatar tsaro na hadin gwiwa, kuma ya shawarci al'umma dasu kasance masu sanya ido cikin wadannan kwanaki masu zuwa, saboda yadda ake samun karuwar bata gari a irin wadannan lokuta.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China