Jerome Korkoya ya shaidawa manema labarai jiya a Monrovia cewa, hukumarsa za ta tabbatar da gudanar da sahihin zabe mai cike da adalci.
A baya, an tsara gudanar da zaben ne a ranar 7 ga watan Nuwamba, amma sai kotun kolin kasar ta bada umarnin dakatarwa, bisa korafin da wasu jam'iyyu suka shigar gabanta bayan kammala zageye na farko a ranar 10 ga watan Oktoba.
A cikin korafin, jam'iyya mai mulki ta Unity da jam'iyyar adawa ta Liberty, sun yi kira da a sake gudanar da zaben. Sai dai, kotun kolin ta yi watsi da bukatar, inda a makon da ya gabata ta dage umarnin dakatarwa da ta bayar.
Zagaye na 2 na zaben, zai gudana ne tsakanin dan takarar jam'iyyar Coalition for Democratic Change George Weah da na Jam'iyyar Unity mai mulki wato Joseph Boakai. (Fa'iza Mustapha)