Miroslav Lajcak, ya bayyana cikin wata tattauanwa da Kamfanin dillancin labarai na Xinhua cewa, Kasar Sin ta riga ta mamaye wani muhimmin mataki a matsayinta na daya daga cikin mambobin dindindin na kwamitin sulhu na MDD, kana ta zama daya daga cikin manyan masu bada gudunmuwa ga kasafin kudi da samar da kudaden raya majalisar.
Ya ce kasar Sin na daya daga cikin kasashen farko da suka rattaba hannu kan yarjejeniyar sauyin yanayi ta Paris, sannan ta yi alkawarin bada dala biliyan 3.1 ga asusun hadin gwiwa na tallafawa kasashen maso tasowa magance sauyin yanayi wato South-South Cooperation Fund, wanda ke matsayin wani muhimmin yunkuri ga kasashe masu tasowa. (Fa'iza Mustapha)