180213-Jakadan-Sin-ya-baiwa-daliban-jamiar-ABU-kyautar-kudin-karatu-Amina.m4a
|
Jakadan ya kuma bayyana cewa, wannan shekara, shekaru 47 ke nan da kulla dangantakar diplomasiyya tsakanin Sin da Nigeria, shi ya sa a wannan lokaci mai muhimmanci na tunawa da wannan dangantaka,kasar Sin ta baiwa wadannan dalibai 47 wannan kyauta ta yadda bangarorin biyu za su habaka hadin gwiwar dake tsakaninsu.
Mista Zhou ya kuma tabo batun taron kolin dandanlin hadin gwiwar Sin da Afrika da za a yi a birnin Beijing a watan Satumba wannan shekara, inda ya ce matasa sune kashin bayan kowa ce kasa, kuma kulla zumunci da dalibai zai taimaka sosai wajen habaka hadin gwiwa tsakanin kasashen biyu nan gaba.
Wakiliyarmu Amina dake Nigeria ta hakarci biki ta kuma zanta da malam Ibrahim Garba shugaban jami'ar ABU, wanda ya bayyana muhimmancin kyautar kudin karatu.