in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin za ta hada kai da masu ruwa da tsaki wajen cimma nasarar taron SCO
2018-02-14 19:04:54 cri
Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Geng Shuang, ya ce Sin za ta ci gaba da kara kaimi wajen cudanya da kasashe mambobin kungiyar hadin gwiwa ta Shanghai ko SCO a takaice.

Da yake tsokaci game da shirin da ake yi, na halartar shugaban kasar Rasha taron na SCO, Mr. Geng ya ce Sin za ta sanya sabon kaimi ga ci gaban kungiyar, tana kuma maraba da zuwan sabon shugaban na Rasha, duba da irin kimar da kasar ke da ita a kungiyar.

Ana dai sa ran gudanar da taron SCO ne a birnin Qingdao cikin watan Yuni na wannan shekara. (Saminu Hassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China