in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sakataren MDD ya bayyana bacin ransa kan harin da aka kai a wata makaranta dake Florida
2018-02-16 12:40:53 cri

Babban sakataren MDD Antonio Guterres ya bayyana bakin cikinsa kan hari da bindiga da wani matashi ya kai ranar Laraba kan wata makarantar sakandare dake garin Parklad a jihar Floridan kasar Amurka.

Mai magana da yawun MDD Stephane Dujarric wanda ya bayyana hakan yayin taron manema labarai ya bayyana cewa, Mr. Guterres ya bayyana hakan ne cikin wata wasika da ya aikewa gwamnan jihar ta Florida Rick Scott da jakadar Amurka a MDD Nikki Haley. Guterres ya ce, abin bakin ciki ne, yadda ake halaka matasa a wuraren da ya kamata a ce dalibai suna da tsaro, a hannu guda kuma aka wargaza iyalai, tare da cusa al'umma baki daya cikin zaman zulumi.

Sakataren na MDD ya ce, a wannan lokaci na bakin ciki, daukacin majalisar na jajantawa iyalan da wannan abin bikin ciki ya shafa.

Kimanin mutane 17 ne, tsohon dalibin makarantar mai shekaru 19 ya halaka, lokacin da ya bude wuta kan dalibai da malamai a makarantar sakandaren ta Marjory Stoneman Douglas dake Parkland a jihar Florida.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China