in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Jama'ar kasar Sin sun taya juna murnar bikin bazara na shekarar 2018
2018-02-16 13:23:17 cri

Yau Juma'a 16 ga watan Fabarairu ce rana ta farko ta sabuwar shekarar kasar Sin bisa kalandar gargajiyar kasar. Al'ummar kasar Sin suna kuma gudanar da bikin baje-koli, da kallon fitilu masu launuka, tare da yawon shakatawa zuwa wurare daban daban da sauransu shagulgula na taya juna murnar bikin bazara na wannan shekara.

Jama'ar kasar Sin na bayyana buri da fatansu a sabuwar shekara, na samun jin dadin zaman rayuwa tare da karin wadata a kasar Sin.

Yau ce ranar farko a sabuwar shekara ta kasar Sin bisa kalandar gargajiya ta kasar. An gudanar da bukukuwa da dama kamar bikin yin baje-koli da yin yawon shakatawa da kallon jerin gwanon motoci masu ado da sauransu.

Mataimakiyar shugabar hukumar harkokin al'adu ta birnin Beijing Pang Wei ta yi bayani cewa, a bana akwai take na wasanni a kan kankara na musamman a cikin bukukuwan yin baje-koli a birnin Beijing, wadanda za su kawo jama'ar birnin damar sanin al'adun wasanni a kan kankara. Pang Wei ta bayyana cewa,

"A bana akwai guda shida cikin manyan bukukuwan baje-koli na birnin Beijing da suke da nasaba da al'adun wasanni a kan kankara, kana an kafa sabon bikin wasanni a kan kankara wanda gwamnatin unguwar Shijingshan ta Beijing, da kwamitin shirya wasannin Olympics na lokacin hunkuru na birnin Beijing suka dauki nauyin gudanar da shi, don maraba da bikin bazara da gasar wasannin Olympics na lokacin hunkuru."

Bikin nuna fitilu masu launuka na Kogin Qinhuai na birnin Nanjing, yana daya daga cikin manyan bukukuwa mafi girma da Sinawa suka fi yawa da halarta. Gu Yeliang, mai gadon wasu al'adun gargajiya ba na kayayyaki ba na kasar Sin wanda ya halarci bikin a wannan karo ya bayyana cewa,

"Gare mu, bikin nuna filitu masu launuka da ake gudanarwa a kowace shekara, abun yabo ne da aka shirya mana, wanda ke sa mana kaimi wajen da samun ci gaba."

Jama'ar kauyen Taigedou dake yankin Mongoliya cikin gida mai cin gashin kansa na kasar Sin, suna taya murnar bikin baraza. A gidan Liu Liying, ta yi amfani da hanyar internet wajen sayar da amfanin gona a cikin shekara da ta gabata, yanzu iyalanta sun samu wadata, tana kuma fatan bude wani dakin sayar da abinci dake kauye a sabuwar shekara. Liu Liying ta ce,

"Zan bude wani dakin sayar da abinci a kauyen mu bayan hutun bikin bazara. Yanzu mutane sun fi son zuwa kauye cin abinci, kana ina son yin amfani da dandalin yanar gizo don sayar da amfanin gonarmu." (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China