in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban Najeriya ya yi Allah wadai da harin da aka kaddamar a wani kauyen arewacin kasar
2018-02-17 13:12:42 cri
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya yi Allah wadai da babbar murya game da harin kisan gilla da aka kaddamar kan al'ummar kauyen Birane a jihar Zamfara dake arewa maso yammacin kasar.

A wata sanarwa wanda kamfanin dillancin labarai na Xinhua ya samu kwafenta, shugaban na Najeriya ya jajantawa iyalan wadanda harin na rashin imani ya rutsa da su, kana wasu da dama suka jikkata.

Shugaban ya umarci ministan tsaron kasar, Mansur Dan Ali, da ya hanzarta bincikar halin da ake ciki, kuma ya sanar da shi yanayin da ake ciki ba tare da bata lokaci ba.

Shugaba Buhari, ya baiwa hukumomin tsaron kasar umarnin hanzarta tura jami'an tsaro yankunan da lamarin ya faru don baiwa al'ummar yankunan kariya, kana su gaggauta binciko wadanda ke da hannu don daukar matakan shari'a kansu.

Ya ce gwamnatinsa ba za ta taba lamintar zubar da jinin al'ummar da ba su ji ba ba su gani ba a duk fadin kasar, sannan ya bukaci jami'an tsaron da su kawo karshen wadannan hare-haren rashin imani.

Wasu shaidun gani da ido sun tabbatar da mutuwar mutane 36, yayin da wasu da dama kuma suka jikkata a lokacin da wasu dauke da makamai suka bude wuta a kauyen Birane a ranar Larabar da ta gabata.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China