in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin ta jaddada kudurinta na kin amfani da makaman nukiliya wajen kai hari
2018-02-18 12:17:11 cri
Wata babbar jami'ar diflomasiyyar kasar Sin Fu Ying, ta ce kasar ta kuduri niyyar tsayawa kan akidarta na kin amfani da makaman nukiliya wajen kai hari, tana mai bayyana damuwa game da hadduran da dake tattare da samar da makaman nukiliya a wannan zamani.

Fu Ying wadda gogaggiyar jami'ar diflomaisyya ce, kuma shugabar kwamitin kula da harkokin waje na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin, ta bayyana haka ne jiya Asabar a wajen babban taron tsaro dake gudana birnin Munich na Jamus.

Ta ce kasarta ta tsaya ne kan mallakar karamar ma'adanar nukiliya, kuma za ta ci gaba da bin tsarin kare kai, kana ba za ta mallaki makaman nukiliya da suka wuce kima ba.

Har ila yau, ta ce kasar Sin ta daura niyyar bin tsarin kin amfani da makamin nukiliya wajen kai hari da kin farwa wata kasa da ta mallaki nukiliyar a kowanne irin yanayi, da kuma kin amfani da shi a yankunan da ba su mallaki makamin ba.

Fu Ying ta ce yana da matukar muhimmanci kasashe 5 mambobin dindindin na kwamitin sulhu na MDD da suka hada da Sin da Amurka da Rasha da Birtaniya da Faransa, su ci gaba da yunkuri tare da daukar alhakin tabbatar da zaman lafiya a duiniya don kare yaduwar makamai da ci gaba da kawar da makaman nukiliya.

Bugu da kari, ta ce kasar Sin na mara baya ga yarjejeniyar haramta gwajin makamin nukiliya. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China