in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin ta ce sake kara hawa teburin sullhu na da muhimmanci wajen warware rikicin nukiliyar Koriya
2018-02-18 12:52:08 cri
Kasar Sin ta ce tana fatan za a sake hawa teburin sulhu don warware batun nukiliyar zirin Koriya dake bukatar daukin gaggawa.

Kasar Sin ta bakin babbar jami'ar diflomasiyyarta kuma shugabar kwamitin kula da harkokin waje na majalisar wakilan jama'ar kasar Fu Ying, ta bayyana haka ne a wajen babban taron tsaro dake gudana a Munich na Jamus, inda ta ce rashin yadda tsakanin Amurka da Koriya ta arewa, ya sa an gaza aiwatar da wata yarjejeniya tsakaninsu, al'amarin da ke kara zaman dar-dar a zirin.

Kasar Sin ta ce tana goyon bayan kawar da makaman nukiliya a zirin Koriya, sannan ta amince da sanya takunkuman da suka dace, tana mai cewa ta bada cikakken goyon baya ga kudurorin kwamitin sulhu na MDD da suka shafi takunkumai kan Korioyar.

Ta kara da cewa, ta lura an samu wata kyakkyawar dama a baya-bayan nan, a lokacin da Koriya ta arewa da takwararta ta kudu suka yi amfani da wasannin motsa jiki na lokacin hunturu na Pyeongchang, a matsayin dandalin tuntubar juna.

Kasar Sin ta ce tana fatan Amurka za ta yi amfani da wannan dama wajen sake hawa teburin sulhu da nufin dawo da zaman lafiya a yankin. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China