Hukumar CNTA ta ce, adadin kudaden shigar hukumar ya karu da kashi 9.9 bisa 100, inda ya kai kimanin yuan biliyan 258.2, kwatankwacin dalar Amurka biliyan 40.69 a cikin kwanakin uku.
Kimanin fasinjoji miliyan 3.85 ne suka yi tafiye tafiye ta jiragen kasa a ranar Jumma'ar da ta gabata, wato ranar farko ta fara hutun na tsawon mako guda na bikin, sama da karin kashi 8.4 bisa 100 a makamanciyar ranar a shekarar bara, a cewar hukumar kula da sufurin jiragen kasa ta kasar Sin CRC.
CRC ta ce, tafiyar gajeren zango ta jiragen kasa ga iyalai ta zama wata al'ada mafi karbuwa a tsakanin al'ummar sinawa sakamakon karin bunkasuwar da aka samu na hadewar yankunan kasar da hanyoyin jiragen kasa masu saurin tafiya.
Da ma dai hukumar CNTA, ta yi hasashen samun Sinawa masu yawon bude ido kimanin miliyan 385 wadanda ake sa ran za su yi bulaguro a lokutan hutun, wato tsakanin ranar 15 zuwa 21 ga watan nan na Fabrairu.(Ahmad Fagam)