Majalisar ministocin kasar ce ta ayyana dokar ta-bacin, tana mai cewa, ta yi hakan ne domin kare kundin tsarin mulkin kasar, da ba da kariya ga al'ummar kasar, da dukiyoyinsu daga fuskantar barazanar tashin hankalin dake wanzuwa a wasu sassan kasar a halin yanzu.
Siraj Fegessa, ministan tsaron Habasha, ya shedawa kafafen yada labaran kasar cewa, dokar ta-bacin da aka kafa za ta shafe tsawon watanni 6 ne, kuma dukkannin jami'an tsaron kasar za su yi aiki tare don tabbatar da ganin dokar tana aiki yadda ya kamata.
Kasar ta biyu mafi yawan jama'a a Afrika ta sha fuskantar dokar ta-baci har na tsawon watanni 10 tun daga watan Oktoban shekarar 2016, biyowa bayan matakin da majalisar dokokin kasar Habashan ta dauka na kara wa'adin watanni 4 daga cikin watanni shidan da aka sanya tun da farko na dokar-ta-bacin.
A cewar Fegessa, dokar-ta-bacin da aka kafa na watanni 10 a kasar ta yi matukar tasiri wajen lafawar tashin hankalin da ya barke a kasar ta gabashin Afrika musamman a cikin shekarar 2016 da 2017.
Fegessa ya nanata cewa za'a cigaba da tsawaita wa'adin dokar-ta-bacin muddin al'amura ba su daidaita ba a kasar.(Ahmad Fagam)