in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shirin gwamnatin kasar Sin na yiwa hukumomin da ma'aikatu gyaran fuska
2018-03-22 12:53:27 cri

A kwanakin baya ne a yayin taro karo na hudu na cikakken zaman farko na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin (NPC) karo na 13 aka saurari daftarin dokar sa ido da na shirin sake fasalin ma'aikatun majalisar gudanarwar kasar, taron da ya samu halartar shugabannin kasar Sin da suka hada da Xi Jinping da Li Keqiang da sauransu.

Manufar gudanar da wadannan gyare-gyare ita ce tabbatar da cewa, gwamnati za ta rika gudanar da ayyukanta bisa doka, da kokarin gamsar da al'ummar kasar. Za kuma a sauya ayyukan gwamnati, don sakarwa kasuwa mara a maimakon gwamnati ta rika kankane komai ta yadda za ta yi cikakken tasiri ga aikin raba albarkatu, da baiwa gwamnati damar taka rawa mai kyau a harkoki daban daban.

Za a yi kokarin samun ci gaban tattalin arziki mai inganci, da marawa gwamnatin kasar baya a kokarinta na sa ido kan harkokin kasuwanni, da kula da al'umma, da samar da hidima ga jama'a, da kiyaye muhalli, da makamantansu.

Tun bayan da kasar Sin ta fara aiwatar da manufar gyare-gyare a cikin gida da bude kofa ga kasashen waje a shekarar 1978, an sauya fasalin majalisar gudanarwar kasar har karo 7, ta yadda hakan ya samar da wani tsarin gwamnati da ya dace da tsarin kasar mai bin tafarkin gurguzu, inda ake samun kasuwanni masu 'yanci. Sai dai bayan wadannan gyare gyare, an dauki lokaci mai tsawo ba a sauya fasalin hukumomin gwamnatin kasar ba tun bayan shekarar 2013.

Haka zalika, cikin shekarun baya, kasar Sin ta kara dora muhimmanci ga yunkurin kyautata muhallin halittun kasar. Sa'an nan don biyan bukatun kasar a wannan fanni, an yi shirin daidaita majalisar gudanarwar kasar don kafa wata sabuwar ma'aikata, wato ma'aikatar albarkatun kasa da ta halittu.

Ban da wannan kuma, sauran sabbin ma'aikatun da ake fatan kafawa a kasar Sin sun hada da ma'aikatar kula da muhallin halittu, wadda za ta gabatar da manufofin kiyaye muhallin halittu, da sa ido kan yunkurin dakile gurbacewar muhalli. Bugu da kari, ana fatan kafa wasu hukumomin da za su rika sanya ido kan harkokin kasuwanni, da hada-hadar kudi, da aikin bankuna da harkar inshora, da hukumar kula da ba da tallafi ga kasashen wajen da hukumar kula da tsoffin sojoji masu ritaya da dai sauransu.

Masana na ganin cewa, wannan mataki zai kara inganta tafiyar da harkokin gwamnati bisa tsarin gurguzu mai sigar musamman na kasar Sin a kokarin da take na tafiya da zamani. (Ahmed, Saminu, Ibrahim/Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China